Wannan bayani na tsare sirri ta shafi shafukan yanar gizo na Microsoft, ayyuka da kuma samfurori da suke tattara bayanai da kuma nuna waɗannan sharuɗɗa, da kuma ayyukan samfurinsu na tallafi. Bai shafi shafukan yanar gizo na Microsoft ba, ayyuka kuma samfurori da ba sa nuna ko hanya ga wannan bayani ko cewa suna da bayanan tsare sirri na kansu.
Karanta taƙaitawar da ke ƙasa a kuma danna "Ƙarin Sani" don bayani a kan wani keɓaɓɓen batu. Haka nan ƙila za ka iya zaɓa daga samfurori da aka jera a sama don duba bayanin tsare sirri na wannan samfuri. Wasu samfurori, ayyuka ko siffofi da aka bayyana a cikin wannan bayani ƙila ba za su samu a duk kasuwanni ba. Za ka iya neman ƙarin bayani a kan jajircewar Microsoft don kare sirrinka a http://www.microsoft.com/privacy.
Mafi yawan shafukan Microsoft suna amfani da "kukis", waɗanda wasu ƙananan fayilolin rubutu ne da sabar yanar gizo za ta iya karantawa a kan yankin da ya sanya kuki a kan rumbun kwamfutarka. Ƙila mu yi amfani da kukis don adana zaɓuɓɓukanka da kuma saituna; taimakawa wajen shiga; samar da talla da aka yi niyya; da kuma nazartar ayyukan shafi.
Haka nan muna amfani da tashoshi na yanar gizo wajen taimakawa isar da kukis da kuma tattara nazari. Ƙila waɗannan su haɗa da tashoshin yanar gizo na wasu, waɗanda aka haramtawa tattara keɓaɓɓen bayaninka.
Kana da kayan aiki da dama na gudanar da kukis da sauran kimiyoyi masu kama, da suka haɗa da:
Amfanin da mu ke da Cookies
Mafi yawan shafukan Microsoft suna amfani da "kukis", waɗanda wasu ƙananan fayilolin rubutu ake sanyawa cikin rumbunka ko wata sabar yanar gizo Kukis sun ƙunshi rubutu ne da sabar yanar gizo za ta iya karantawa a kan yankin da ya samar maka da kuki. Wannan rubutu yana ƙunsar wani layi na lambobi da kuma haruffa da suke gane kwamfutarka, amma ƙila su ƙunshi wasu bayanai ma. Ga misalin rubutun da aka adana a cikin cookie wadanda Microsoft zai iya ajiyewa a kan babban faifanka yayin da ka ziyarci daya daga shafukan intanet din mu: E3732CA7E319442F97EA48A170C99801
Za mu iya amfani da cookies don:
An jera wasu da cikin cookies din da muke yawan amfani da su a cikin wannan jadawali. Wannan jeri ba iyakarsa kenan ba, amma ana nufi fasalta wasu daga dalilan da muke saita cookies. Idan ka ziyarci daya daga cikin shafukan intanet dinmu, shafin zai iya saita wasu ko duk wadannan cookies:
Baya ga kukis da ƙila Microsoft za ta saita a yayin da ka ziyarci shafukanmu na gizo, ƙila wasu kamfanoni su saita wasu kukis a kan rumbun kwamfutarka idan ka ziyarci shafukan yanar gizo. A wasu lokuta, dalili shi ne saboda mun yi hayar kamfanin ne don ya samar mana da wasu ayyuka a madadinmu, misali nazartar shafi. A wasu lokutan, saboda shafukan yanar gizo namu sun ƙunshi ƙunshiya ko talla daga wasu kamfanoni, kamar bidiyoyi, ƙunshiyar labara ko talla da wasu hanyoyin sadarwar suke isarwa. Saboda mai bincikenka tana haɗi da waɗannan kamfanoni, sabobin yanar gizo don dawo da wannan ƙunshiya, waɗannan kamfanoni suna samun damar saita ko karanta kukis ɗinsu a kan rumbun kwamfutarka.
Yadda za ka Sarrafa Cookies
Alal misali, a cikin Internet Explorer 9, ƙila ka iya toshe kukis ta bin matakan da suke tafe:
Umurnai na toshe kukis a cikin wasu masu bincike suna samuwa a http://www.allaboutcookies.org/manage-cookies/.
Kula cewa idan ka zabi ka toshe cookies, ba lalle ne ka iya shiga ko yin amfani da sauran siffofin cudanya na shafuka da aiyukan Microsoft da suke dogara da cookies ba, da kuma wasu zabukan talla da ke dogara da cookies ba za a iya kiyaye su ba.
Alal misali, a cikin Internet Explorer 9, ƙila za ka iya share kukis ta bin matakan da suke tafe:
Za a iya samun bayanan share cookies a cikin sauran mashigan-intanet a http://www.allaboutcookies.org/manage-cookies/.
Kula cewa idan ka zabi ka share cookies, za a share duk wasu saituka da zabuka da wadancan cookies ke sarrafawa, da suka hada da zabukan talla, kuma ba lalle ne a sake kirkirarsu ba.
Sarrafawar Mai Bincike "Kada a Bi-sawu" da kuma Kariyar Bin-Swu. Wasu sababbin mashigan-intanet sun game siffofin "Kada Ka Bibiya". Yawancin wadannan siffofin, yayin da aka kunna su, suna aika sigina ko zabi zuwa ga shafukan intanet da ka ziyarta suna nuni da cewa ba ka son a bibiyeka. Wadannan shafukan intanet (ko wasu matani daban akan wadannan shafukan intanet) kan iya ci gaba da aiwatar da harkoki da za ka iya dauka a matsayin bibiya koda kuwa ka bayyana wannan zabi, ya danganta ga aiyukan sirri na shafukan intanet din.
Internet Explorer 9 da 10 suna da siffa da aka kira Kariyar Bibiya da ke taimakawa wajen hana shafukan intanet din da ka je aikawa da cikakkun bayanai game da ziyararka kai tsaye zuwa ga wasu masu samar da matani na daban. Yayin da ka kara Jerin Kariyar Bibiya, Internet Explorer za ta toshe matanin wasu daban, da suka hada da cookies, daga kowane shafin intanet da aka jera a matsayin shafin intanet da za a toshe. Ta hanyar takaita kira zuwa wadannan shafukan intanet, Internet Explorer za ta takaita bayani da wadannan shafukan intanet na daban za su iya tattarawa game da kai. Kuma yayin da ka ke da damar Jerin Kariyar Bibiya, Internet Explorer za ta aika da siginar Kada Ka Bibiya ko zabi zuwa ga shafukan intanet din da ka ziyarta. Kari dai, a cikin Internet Explorer 10 zza ka iya "kashewa" ko "kunna" DNT a daban daban, idan kana so. Don ƙarin bayani a kan Jere-jeren Kare Bin-Sawu da Kada Ka Bibiya, duba bayanin tsare sirri na Internet Explorer ko Taimakon Internet Explorer.
Ɗaiɗaikun kamfanonin talla ƙila su samar da nasu damar na dainawa tare da ƙarin zaɓuɓɓukan talla masu zurfi. Alal misali, zaɓin talla na Microsoft da kuma dainawa yana samu a http://choice.live.com/advertisementchoice/. Lura cewa dainawa ba ya nufin ɗewa za ka dakatar da samun talla ko ganin talla kaɗan; koda yake, idan ka daina, tallan da ka karɓa ba zai zama wanda aka yi niyya ba. Kari akan haka, fita-daga ba ya hana bayani zuwa sabarmu, amma yana dakatar da kirkirarmu ko sabunta bayanan mutane wadanda akan iya amfani da su don tallar halayya.
Amfanin da mu ke da Tutocin Intanet
Shafukan intanet na Microsoft kan kunshi hotunan lantarki da aka fi sani da tutocin intanet - wadansu lokutan akan kira su da zubin kwayar-hoto - wadanda za a iya amfani don taimakawa kaiwa cookies akan shafukanmu na intanet, bari mu kidaya masu amfani da suka ziyarci wadancan shafuka kuma suka kai aiyukan gamayyar-suna. Ƙila mu haɗa da tashoshin yanar gizo a cikin saƙonnin garaɓasarmu na imel ko wasiƙun labarai don ƙayyadw ko an buɗe saƙonnin kuma kuma an amsa su.
Haka kuma za mu iya aiki da sauran kamfanoni da ke yin talla a shafukan intanet na Microsoft don ajiye tutocin intanet akan shafukansu na intanet ko a cikin tallace tallacensu don ba mu damar gina kididdiga akan yadda yawanci danna kan talla a shafin intanet na Microsoft kan haifar da sakamakon saye ko sauran aiyuka akan shafin intanet na mai talla.
Daga ƙarshe, shafukan Microsoft ƙila sun ƙunshi tashoshin yanar gizo daga wasu kamfanoni don taimakawa wajen tara wasu alƙalima da ya shafi amfani na kamfen garaɓasarsmu ko sauran ayyukan shafin yanar gizo. Waɗannan tashoshin yanar gizo ƙila su ƙyale wasu kamfanoni su saita ko karanta wani kuki a kan kwamfutarka. Mun haramtawa wasu kamfanoni amfani da tashoshin yanar gizo a kan shafukanmu don tattara ko samun dama ga keɓaɓɓen bayaninka. Koda yake, ƙila ka sami damar damar ficewa daga tattara bayanai ko amfani da waɗannan kamfanonin nazari ta danna hanyoyin ga kowane masu samar da nazari da suke tafe:
Sauran Kimiyoyi Masu Kama
Baya ga daidaitattun kukis da kuma tashoshin yanar gizo, shafukan yanar gizo za su iya amfani da sauran kimiyoyi don adana da kuma karanta fayilolin bayanai a kan kwamfutarka. Ƙila za a yi wannan ne don barin zaɓuɓɓukanka ko don haɓaka gudu da kuma ƙarfin aiki ta adana wasu fayoiloli a gida. Amma, kamar daidaitattun kukis, haka nan za a iya amfani da wani farɗan mai ganowa don kwamfutarka, wanda sannan za a yi amfani da shi waen bin-sawun halayyarka. Waɗannan kimiyoyi sun haɗa da Abubuwan Rabawa na Gida (ko "Kukis masu walƙiya") da kuma Aikace-aikacen Maájiya na Silverlight.
Abubuwan Rabawa na Gida ko "Kukis masu walƙiya." Shafukan yanar gizo da suke amfani da kimiyoyin Adobe ƙila su yi amfani da Abubuwan Rabawa na Gida ko "Kukis masu walƙiya" don adana bayanai a kan kwamfutarka. Lura cewa samuwar share kukis masu Filasha ƙila saitin mai binciken ya iya ko ba zai iya sarrafawa shi ba ga daidaitattun kukis saboda ƙila ya bambanta daga mai bincike zuwa wata. Don gudanar ko toshe kukis masu Filasha, tafi http://www.macromedia.com/support/documentation/en/flashplayer/help/settings_manager.html.
Aikace-aikacen Maájiya na Silverlight. Shafukan yanar gizo ko aikace-aikace da suke amfani da kmiyar Microsoft Silverlight ƙila su sami damar adna bayanai ta amfani da Aikace-aikacen Maájiya na Silverlight. Don koyon yadda za ka gudanar ko toashe wannan maájiya, ziyarci Silverlight.
Microsoft tana karɓar nauóín bayanai don sarrafawa yadda ya kamata da kuma samar maka samfurori mafi kyau, ayyuka da kuma gogewa da za mu iya.
Muna karɓar bayani idan ka yi rajista, shiga da kuma amfani da shafukanmu da kuma ayyuka. Haka nan ƙila mu sami bayani daga wasu kamfanoni.
Mun karɓi wannan bayani a cikin hanyoyi mabambanta, da suka haɗa da fam-fam na yanar gizo, kimiyoyi kamar kukis, shiga yanar gizo da kuma manhaja a kan kwamfutarka ko wata naú ra.
Microsoft tana karɓar nauóín bayanai don sarrafawa yadda ya kamata da kuma samar maka samfurori mafi kyau, ayyuka da kuma gogewa da za mu iya. Wasu daga cikin wannan bayani da ka samar kai tsaye gare mu. Muna samun wasu daga cikinsu ne ta lura da yadda kake hulɗa tare da samfurorinmu da kuma ayyuka. Wasu daga cinkinsa suna samuwa ne daga sauran tushe da ƙi;a muke haɗewa tare da bayanai da muka tattara kai tsaye. Ba tare da laákari da tushen ba, mun ti imani yana da muhimmanci mu kula da wannan bayani da kuma taimka maka riƙe sirrinka
Abin da muke karɓa
Yadda muka karɓa:
Muna amfani da hanyoyi da dama da kuma kimiyoyi don tara bayani game da yadda kake amfani da shafukanmu da kuma ayyuka, kamar:
Microsoft na amfani da bayanin da muka tattara don gudanarwa, haɓakawa da kuma keɓance samfurori da kuma ayyuka da muke samarwa.
Haka nan ƙila za mu yi amfani da bayanin wajen sadarwa tare da kai, alal misali sanar da kai game da asusunka da kuma ɗaukakawar tsaro.
Kuma ƙila mu yi amfani da bayanin don taimakawa wajen sa tallan da ka gani a kan ayyukan tallafin tallarmu don ya ƙara zama ya dace.
Microsoft na amfani da bayanin da muka tattara don gudanarwa, haɓakawa da kuma keɓance samfurori da kuma ayyuka da muke samarwa. Bayanin da aka tattara ta hanyar ɗaya daga cikin ayyukan Microsoft ƙila a haɗe shi da bayanin da aka tattara ta sauran ayyukan Microsoft don ba ka ƙarin daidaito da kuma keɓaɓɓiyar gogewa a cikin hulɗarka tare da mu. Haka nan ƙila mu haɗo wannan tare da wani bayani daga sauran kamfanoni. Alal misali, ƙila mu yi amfani da ayyukan daga sauran kamfanoni don taimaka mana samar da wani babban yanki ta laákari da adireshin IP ɗinka don keɓance wasu ayyuka ga yankinka.
Haka nan ƙila mu yi amfani da bayanin don sadarwa tare da kai, alal misali sanar da kai idan idan rajistarka za ta ƙare, sanar da kai lokacin da ɗaukawar tsaro ta samu ko sanar da kai lokacin da za ka ɗauki mataki don barin asusunka aiki.
Microsoft na samar da mafi yawan shafukanmu da kuma ayyuka kyauta saboda talla ne yake tallafa masu. Don damar samar da waɗannan ayyuka samuwa koína, ƙila mu yi amfani da bayanin da muka tattara wajen taimakawa haɓaka tallace-tallace da ka gani ta samar da su su dace da kai.
Ban da kawai kamar yadda aka bayyana a cikin wannan bayanin tsare sirri, ba za mu bayyana keɓaɓɓen bayaninka ba ga wani ba tare da yardarka ba.
Duba Sauran Muhimmin Bayanin Tsare Sirri don ƙarin bayani game da lokacin da muke bayyana bayaninka, haɗe da rassan Microsoft da kuma masu aiki, idan doka ta buƙata ko don amsa wani kira na doka; don yaƙar zamba ko kare kanmu; ko kare rayuka.
Danna nan don ƙarin bayani a kan rabawa ko bayyana keɓaɓɓen bayani:
Wasu ayyukan Microsoft suna ba ka damar duba ko gyara keɓaɓɓen bayaninka a kan layi. Don kare wasu daga duba keɓaɓɓen bayaninka, za a buƙaci ka shiga tukuna, Yadda za ka sami dama ga keɓaɓɓen bayaninka zai danganci shafuka ko ayyukan da ka yi amfani da su.
Microsoft.com - Za ka iya samun dama da kuma ɗaukaka furofayil ɗinka a kan microsoft.com ta ziyartar Cibiyar Furofayil ta Microsoft.com.
Lissafin Kuɗi na Microsoft da kuma Ayyukan Asusu- Idan kana da wani Lissafin Kuɗi na Microsoft, za ka iya ɗaukaka bayaninka a shafin Lissafin Kuɗi na Microsoft ta danna kan hanyoyin "Keɓaɓɓen Bayani" ko "Bayanin Lissafin Kuɗi".
Haɗin Microsoft - Idan ka yi rajistar amfani da Haɗin Microsoft, za ka iya samun dama da kuma gyara keɓaɓɓen bayaninka ta danna Gudanar da Furofayil ɗinka na Haɗi a shafin yanar gizo na Haɗin Microsoft.
Windows Live - Idan ka yi amfani da ayyukan Windows Live, za ka iya ɗaukaka bayanin furofayil ɗinka, canza kalmar sirri, duba farɗan ID da ya danganci takardun shaidarka, ko rufe wasu asusu-asusu ta ziyartar Windows Live Ayyukan Asusu.
Furofayil ɗin Jamaána Windows Live - Idan ka ƙirƙiri wani furofayi na jamaáa kan Windows Live, ƙila ka iya gyara ko share bayanin a cikin furofaayil ɗinka ba jamaáta zuwa furofayil na Windows Live ɗinka.
Neman Talla - Idan ka nema talla ta hanyar Talla na Microsoft Advertising, za ka iya yin bita da kuma gyara keɓaɓɓen bayaninka a kan shafin yanar gizo na Microsoft adCenter.
Shirye-shiryen Abokin Hulɗa na Microsoft - Idan ka yi rajista tare da Shirye-shiryen Abokin Hulɗa na Microsoft, za ka iya yin bita da kuma gyara furofayil ɗinka ta danna Gudanar da Asusunka a kan yanar gizo na Shirin Abokin Hulɗa.
Xbox - Idan kai mai amfani ne da Xbox LIVE ko Xbox.com user, za ka iya yin bita ko gyara keɓaɓɓen bayaninka, da ya haɗa da lissafin kuɗi da kuma bayanin asusu, saitunan tsare sirri, kariya ta kan layi da kuma zaɓuɓɓukan raba bayanai ta samun dama ga My Xbox a kan naú rar Xbox 360 ko a kan shafin yanar gizo na Xbox.com. Don bauanin asusu zaɓi My Xbox, Asus-asusu. Don wasu saitunan keɓaɓɓen bayani, zaɓi My Xbox, sannan kuma Furofayil, sannan Saitunan Kariyar Kan Layi.
Zune - Idan kana da wani asusun Zune ko rajistar Wucewa na Zune, za ka iya duba da kuma gyara keɓaɓɓen bayaninka a Zune.net (shiga, sami dama ga alamarka ta Zune sannan Aausu nawa) ko ta hanyar manhajar Zune (shiga, sami dama ga alamarka ta Zune, sannan ka zaɓi furofayil na Zune.net).
Idan ba za ka iya samun dama ga keɓaɓɓen bayaninka da shafukan Microsoft suka tattara ko ayyuka ta hanyar hanyoyin da suke sama ba, ƙila waɗannan shafuka da kuma ayyuka su samar maka wasu hanyoyi na samun dama ga bayananka. Za ka iya tuntuɓar Microsoft ta amfani da fam na yanar gizo. Za mu amsa buƙatunka na samun dama ko share keɓaɓɓen bayaninka cikin kwanaki 30.
Idan shafin Microsoft ko sabis ya tattara bayani game da shekara, zai toshe masu amfani ƴan ƙasa da shekara 13 ko su sami izini daga iyaye ko mia kula da su kafin yaro ya yi amfani da shi.
Idan an bayar da izini, ana kulawa da asusun yaron kamar yadda ake kulawa da na kowa, haɗe da samun dama ta sadarwa tare da sauran masu amfani.
Iyaye za su iya canza ko soke izinin kamar yadda aka bayyana a cikin wannan bayanin tsare sirri.
Idan wani shafin yanar gizo na Microsoft ko sbis ya tattara bayanin shekara, ko dai ya toshe masu amfani ƴan ƙasa da shekara 13 ko ya umarce su da su samar da izini daga iyaye ko mai kula da su kafin su yi amfani da shi. Ba za mu tambayi yara ƴan ƙasa da shekara 13 a sane ba su samar da ƙarin bayani da yama wajibi don samar da sabis ɗin ba.
Idan an bayar da izini, ana kulawa da asusun yaron kamar yadda ake kulawa da na kowa. Ƙila yaron ya sami dama ga sadarwar ayyuka kamar imel, saƙon nan-take da kuma allon saƙo na kan layi kuma ƙila ya sami damar sadarwa tare da sauran masu amfani bisa rashin laákari da shekaru.
Iyaye za su iya canza ko soke izinin da suka bayar a da, da kuma bita, shirya ko buƙatar share keɓaɓɓen bayanin ƴaƴansu. A kan Windows Live, iyaye za su iya ziyartar Asusunsu, da kuma danna kan "Izinin Iyayr".
Mafi yawan tallace-tallace na kan layi a kan shafukan Microsoft da kuma ayyuka Tallan Microsoft ne yake nuna su. A yayin da muka nuna maka tallace-tallace na kan layi, za mu sanya kukis ɗaya ko sama domin gane kwamfutarka idan mun nuna maka wani talla. A tsawon lokaci, ƙila mu tara bayani daga shafukan da muke nuna talla kuma mu yi amfani da wannan bayani don taimkawa wajen samar da tallace-tallace masu alaƙa.
Za ka iya daina karɓar talla daga Tallan Microsoft ta ziyartar shafinmu na dainawa.
Mafi yawan shafukanmu na yanar gizo da kuma ayyuka na kan layi talla ne yake tallafa musu.
Mafi yawan tallace-tallace na kan layi a kan shafukan Microsoft da kuma ayyuka Tallan Microsoft ne yake nuna su. A yayin da muka nuna maka tallace-tallace na kan layi, za mu sanya kukis ɗaya ko sama marar ɓacewa domin gane kwamfutarka idan mun nuna maka wani talla. Saboda muna samar da tallace-tallace a kan shafukan yanar gizo na kanmu da ma na abokan hulɗarmu da masu ɗabí, mun sami damar tara bayanai na tsawon lokaci game da nauóín shafuka, ƙunshiya da kuma talla da kai, ko sauran mutane masu amfani da kwamfutarka, suka ziyarta ko duba. Ana amfani da wannan bayani bisa dalilai da dama, misali, yana taimaka mana wajen tababtar da cewa ba ka ga tallace-tallace iri ɗaya ba sau da dama. Haka nana muna amfani da wannan bayani don taimakawa wajen zaɓi da kuma nuna tallace-tallace da aka yi niyya da muka yi imani zai ba ka shaáwa.
Za ka iya daina karɓar talla daga Tallan Microsoft ta ziyartar shafinmu na dainawa. Don ƙarin bayani game da yadda Tallan Microsoft yake tattara da kuma amfani da bayanai, ziyarci Bayanin Dokar Tsare Sirri na Tallan Microsoft.
Haka kuma muna ƙyale wasu kamfanonin talla da suka haɗa da hanyoyin sadarwa na talla nuna tallace-tallace a kan shafukanmu. A wasu lokuta, waɗannan kamfanoni su ma suna sanya kokis a kan kwamfutarka. Waɗannan kamfanoni a halin yanzu suna haɗa da, amma ban da iyakancewa da: 24/7 Real Media, adblade, AdConion, AdFusion, Advertising.com, AppNexus, Bane Media, Brand.net, CasaleMedia, Collective Media, InMobi, Interclick, Jumptap, Millennial Media, nugg.adAG, Mobclix, Mojiva, SpecificMedia, Tribal Fusion, ValueClick, Where.com, Yahoo!, YuMe, Zumobi. Ta yiwu waɗannan kamfanoni su samar da wata hanya ta daina tallan da aka y niyya bisa laákari da kukis ɗinsu. Ƙila ka sami ƙarin bayani ta danna kan sunayen kamfani da yake sama da kuma bin hanyoyin na zuwa shafukan yanar gizo na kowane kamfani. Mafi yawa daga cikinsu mambobi ne na Network Advertising Initiative ne ko Digital Advertising Alliance, wanda kowane daga cikinsu yake samar da hanya mai sauƙi na daina tallace daga kamfanoni da suke ciki.
Za ka iya dakarar da isar da imel na garaɓasa na gaba daga shafukan Microsoft da kuma ayyuka ta bin wasu umurnai keɓaɓɓe a cikin imel ɗin da ka karɓa. Ya dogara da sabis da ake magana, ƙila ka sami zaɓi na yin zaɓuɓɓuka game da karɓar imel na garaɓasa, kiran tarho, da kuma aika mail ga wasu keɓaɓɓun shafukan yanar gizo na Microsoft ko ayyuka.
Idan ka karɓi imel na garaɓasa daga gare mu kuma kana son dakatar da samun su a gaba, za ka iya yin haka ta bin umarnai a cikin wannan saƙo.
Ya dogara da sabis da ake magana, ƙila ka sami zaɓi na yin zaɓuɓɓuka game da karɓar imel na garaɓasa, kiran tarho, da kuma aika mail ga wasu keɓaɓɓun shafukan yanar gizo na Microsoft ko ayyuka ta ziyarta da kuma shiga shafukan da suke tafe:
Waɗannan zaɓuɓɓuka ba su shafi nuna tallarmu na kan layi ba: waiwaya ɓangaren "Nuna Talla (Dainawa)" don ƙarin bayani game da wannan. Haka nan kuma ba su shafi karɓar sadarwar sabis ta wajibi ba da ake kallo a matsayi wasu ayyukan Microsoft, wanda ƙila za ka riƙa karɓa lokaci-lokaci sai dai idan ka soke sabis ɗin.
Asusun Microsoft (wanda a da ake kira Windows Live ID da Microsoft Passport) wani sabis ne da yake ba ka damar shiga samfurorin Microsoft, shafukan yanar gizo da kuma ayyuka, da kuma na abokan hulɗa da Microsoft ta zaɓa. Idan ka ƙirƙiri wani asusun Microsoft, muna umartarka da ka samar da wasu bayanai. A yayin da ka shiga wani shafi ko sabis ta amfani da asusunka na Micrsoft, muna karɓar wani bayani don tabbatar da shaidarka a madadin shafin ko sabis, don kare ka daga amfani da asusu mai cutarwa, da kuma kare yadda ya dace da kuma tsare na sabis ɗin asusun Microsoft. We also send certain information to a site or service you have signed into with your Microsoft account.
Don duba ƙarin bayanai game da asusun Microsoft, da suka haɗa da yadda za ka ƙirƙiri da kuma amfani da wani asusun Micrsoft, yadda za ka gyara bayanin lissafi, da kuma yadda muke tattara da kuma amfani da suka shafi asusun Microsoft, danna kan Ƙara sani.
Asusun Microsoft (wanda a da ake kira Windows Live ID da Microsoft Passport) wani sabis ne da yake ba ka damar shiga samfurorin Microsoft, shafukan yanar gizo da kuma ayyuka, da kuma na abokan hulɗa da Microsoft ta zaɓa. Wannan ya haɗa da samfurori, shafukan yanar gizo da kuma ayyuka misalin waɗanda suke tafe:
Ana ƙirƙirar wani asusun Microsoft.
Za ka iya ƙirƙirar wani adireshin imel a nan ta samar da wani adireshin imel, wata kalmar sirri da kuma sauran, "shaidun asusu", kamar misalin adireshin imel na zaɓi, wata lambar waya, da wata taambaya da kuma amsar sirri. Za mu yi amfani da "shaidun asusunka" don dalilai na tsaro kawai - alam misali, don tabbatar da shaidarka a yayin da ba za ka iya samun dama ga asusunka na Microsoft da kuma buƙatar taimako, ko don saita kalmarka ta sirri idan ba za ka iya samun dama ga adireshin imel da ya shafin asusunka na Microsoft ba. Wasu ayyuka ƙila su buƙaci ƙarin tsaro, a kuma waɗannan lokuta, ƙila a umarce ka da ka ƙirƙiri ƙarin maɓallin tsaro. Wannan adireshin imel da kuma kalmar sirri da ka yi amfani da su wajen rajistar asusun Microsoft su ne "takardun shaidarka" da za ka yi amfani da wajen gaskatawa tare da hanyar sadarwarmu. Bugu-da-ƙari, za a sanya farɗan lambar ID ta 64-bit ga takardun shaidarka kuma za a yi amfani da su wajen gano takardun shaidarka da kuma bayani da ya shafa.
Idan ka ƙirƙiri wani asusun Microsoft, haka nan za mu umarce ka da ka samar da bayanin alƙaluman da suke tafe: jinsi, ƙasa, ranar haihuwa; da kuma adireshin gidan waya. Ƙila mu yi amfani da ranar haihuwa don tabbatar da cewa yara sun sami dama da ta dace daga iyaye ko mai kula da su don amfani da asusun Microsoft kamar yadda doka ta gida ta buƙata. Baya ga wannan, naú rorin tallarmu na kan layu suna amfani da wannan alƙaluma don samar maka da keɓaɓɓen tallace-tallace game da samfurori da kuma ayyuka da ƙila za ka same su masu amfani, amma naú rorin tallarmu ba sa taɓa samun sunanka ko bayanin tuntuɓa. A wani batun kuma, naírƙrin tallarmu ba sa ƙunsar ko amfani da duk wani bayani da zai iya a keɓance da kuma shafarka kai tsaye ba (misali sunanka, adireshin imel da kuma lambar waya). Idan ka fi son kar ka karɓi keɓaɓɓen talla, za ka iya rajistar zaɓinka tare da asusun Microsoft ta ziyartar wannan shafi saboda a duk lokacin da ka shiga shafukan yanar gizo ko ayyuka tare da asusunka na Microsoft, naú rorin tallarmu ba za su samar maka da keɓaɓɓen talla ba. Don ƙarin bayani game da yadda za ka yi amfani da bayani don talla, duba Ƙarin Tsare Sirri na Tallan Microsoft.
Za ka iya amfani da wani adireshin imel da Microsoft ta samar (misali waɗanda suka ƙara da live.com, hotmail.com, ko msn.com) ko wani adireshin imel da wani ya samar (misali masu ƙarewa da gmail.com ko yahoo.com) a yayin rajistar asusunka na Microsoft.
Bayan ƙirƙirar wani asusun Microsoft, za mu aiko maka da wani imel na umartarka da ka tabbatar da cewa kaine mai wannan adireshin imel da ya shafi asusunka na Microsoft. An shirya wannan ne don ya tabbatar da inganci na adireshin imel da kuma taimakawa kare amfani adiresoshin imel ba tare da izinin masu su ba. Bayan nan, za mu yi amfani da adireshin imel ɗin don aika maka sadarwa da ta shafin amfaninka da samfurori da kuma ayyuka na Microsoft; haka nan kuma ƙila mu aiko maka da imel na garaɓasa game da samfurori da ayyuka na Microsoft kamar yadda dokar gida ta ba da dama. Don bayani game da gudanar da rasiɗi na sadarwar garaɓasa, ziyarci Sadarwa.
Idan ka yi ƙoƙarin yin rajistar wani asusun Microsoft kuma ka sami cewa wani tuni ya ƙirƙiri takardun shaida tare da adireshin imel ɗinka a zaman sunan mai amfani, za ka iya tuntuɓarmu da kuma buƙatar mutumin ya canza wani sunan mai amfani saboda ƙila za ka iya amfani da adireshin imel ɗinka a yayin ƙirƙirar takardun shaidarka.
Ana shiga manhaja, shafuka ko ayyuka tare da asusunka na Microsoft.
A yayin da ka shiga wani shafi ko sabis ta amfani da asusunka na Micrsoft, muna karɓar wani bayani don tabbatar da shaidarka a madadin shafin ko sabis, don kare ka daga amfani da asusu mai cutarwa, da kuma kare yadda ya dace da kuma tsare na sabis ɗin asusun Microsoft. Alal misali, idan ka shiga, sabis na asusun Microsoft yana karɓa da kuma ajiye takardun shaidarka da kuma sauran bayani, kamar farɗan lambar ID ta 64-bit ga takardun shaidarka, siga da kuma lokaci da rana. Haka nan, idan ka yi amfani da asusun Microsoft wajen shiga cikin wata naú ra ko cikin manhaja da aka sanya a kan wata naú ra, ana sanya farɗan ID da kai ga naú rar; za a aika wannan farɗan ID da ka a zaman wani ɓangare na takardun shaidarka ga sabis na asusun Microsoft idan ka shiga wani shafi ko sabis daga baya tare da asusunka na Microsoft. Sabis na asusun Microsoft yana aika bayanin da yake tafe ga shafi ko sabis da ka shiga: wani farɗan lambar ID da take ba wa shafin ko sabis dama na ƙayyade ko kai ɗaya ne daga lokaci na shiga zuwa na gaba; lambar siga da aka sa wa asusunka (wata sabuwar lamba da ake sa wa kowane lokaci da ka canza bayaninka na shiga); ko dai an tabbatar da adireshin imel ɗinka; da kuma ko dai an kashe asusunka.
Shafukan wasu da kuma ayyuka da suke ƙyale ka ka shiga tare da asusunka na Microsoft suna buƙatar adireshin imel ɗinka don su samar maka ayyukansu. A waɗannan lokuta, idan ka shiga, Microsoft za ta samar da adireshin imel ɗinka amma ba kalmarka ta sirri ba ga shafin ko sabis. Koda yake, idan ka ƙirƙiri takardun shaidarka tare da shafin ko sabis ɗin, ƙila ya kasance yana da dama mai iyaka ga bayanin da ya shafi takardun shaidarka don taimaka maka sake saita kalmarka ta sirri ko samar da wasu ayyuka na tallafi.
Idan ka karɓi asusunka daga wani kamfani, kamar makaranta, kasuwanci, mai samar fa sabis na intanet, ko mai gudanarwa na wani yanki da ake gudanarwa, ƙila wannan kamfani ya zama yana da hakki a kan asusunka, da ya haɗa da samuwa na sake saita kalmarka ta sirri, duba amfani da asusunka ko bayanan furofayil, karanta ko adana ƙunshiya a cikin asusunka, da kuma dakatar ko soke asusunka. A waɗannan lokuta, za ka bi Yarjejeniyar Sabis na Microsoft da kuma duk wasu ƙarin sharuɗɗa na amfani daga wannan kamfani. Idan kai mai gudanarwa ne na wani yanki da ake gudanarwa kuma ka samarwa masu amfani naka asusu-asusun Microsoft, kai ke da alhaki na duk aiki da yake faruwa a cikin waɗannan asusu-asusu.
Lura cewa shafukan da kuma ayyukan da suke ba ka damar shiga tare da asusunka na Microsoft za su iya amfani ko raba adireshin imel ɗinka ko sauran keɓaɓɓen bayani da ka samar musu a kamar yadda aka bayyana a bayanin tsare sirrinsu. Koda yake, za su iya raba wani farɗan lambar ID da sabis ɗin asusun Microsoft ya samar musu tare da wani kawai don cika wani sabis ko hulɗa da ƙila ka buƙata. Duk shafuka ko ayyukan da suke amfani da asusun Microsoft ana buƙatar su buga bayanin tsare sirri, amma ba ma sarrafa lƙ sa-ido ayyukan tsare sirri na waɗannan shafuka, kumma ayyukan tsare sirrinsu zai bambanta. Za ka yi bitar bayanin tsare sirri a niste na kowane shafi da ka shiga ko sabis ya yi amfani da bayanin da ya tattara.
Za ka iya samun dama ga keɓaɓɓen bayaninka ta zuwa asusu. Za ka iya canja sunanka na mai amfani idan asusunka na Microsoft ba na yanki ne da ake gudanarwa ba. Za ka iya canza kalmarka ta sirri a ko yaushe,adireshin imel na musaya, lambar waya, da kuma tambaya da amsar sirri. Haka nan ƙila ka rufe asusunka na Microsoft ta zuwa asusu, sannan kuma da "Rufe asusunka." Idan wani yanki ne yake gudanar da asusunka, kamar yadda aka bayyana a sama, ƙila a sami wata hanya ta musannan ta rufe asusunka. Lura cewa idan kai mai amfani ne da MSN ko Windows Live, idan ka je asusu, ƙila a miƙa ka zuwa asusu na waɗannan shafuka.
Ƙarin bayani game da asusun Microsoft shafin yanar gizo na asusun Microsoft.
Kara sani game da
A kasa za ka sami karin bayanin sirri da zai yi maka (ko ba zai yi maka) amfani. Da yawan wannan yana bayyana ayyukan gama-gari da mu ke son ka sani amma kada yi zaton dole a bayyana shi a kowane daga bayanan sirrinmu. Kuma wani daga wannan kawai yana nuna zahiri ne (misali, za mu bayyana bayani yayin da doka ta bukace shi), amma koda yake lauyiyinmu suke sa wa mu fade shi. Ka sa a ranka cewa wannan ba cikakken bayani na ayyukanmu - wanann shi ne duk ƙari ga wannan zuwa ga wani ƙarin keɓaɓɓen saƙo da yake cikin bayanan sirri ga kowane samfurin Microsoft da kuma sabis da ka yi amfani da shi.
A kan Wannan Shafin:
Rarrabawa ko Bayyana Bayanan Mutum
Kari akan duk wata rarrabawa da aka bayyana a bayanan sirri don haja ko aikin da ka ke amfani da shi, Microsoft zai iya rarrabawa ko bayyana bayanan mutum:
Haka kuma za mu iya rarraba ko bayyana bayanin mutum, da ya hada da matanin sadarwarka:
Lura cewa shafukan intanet dinmu za su iya hadawa da rariyoyi zuwa wasu shafukan na daban wadannan harkokin sirrinsu kan bambanta da na Microsoft. Idan ka bayar da bayanin mutum ga kowane daga wadancan shafukan intanet, bayaninka zai zama a karkashin bayanan sirri da ke kan wadancan shafukan intanet. Muna baka shawarar da ka duba bayanan sirri na kowane shafin intanet da ka ziyarta.
Kare Tsaron Bayanin Mutum
Microsoft ya kudurci kare tsaron bayananka na mutum. Muna amfani da nau'o'in fasahohin tsaro da hanyoyin dabaru don taimakawa wajen kare bayanka na mutum daga damar marasa izini, amfani ko bayyanawa. Misali, muna adana bayanin mutum da ka samar akan injinan kwamfuta da ke da takaitacciyar damar shiga kuma suke cikin kayan aikin sarrafawa. Yayin da muka tura bayanin mai matukar sirri (kamar lambar katin banki ko kalmar-shiga) ta cikin intanet, muna kare shi ta hanyar amfani da rufewa, kamar ka'idar Shimfidar Soket Mai kariya.
Idan aka yi amfani da kalmar-shiga don taimakawa wajen kare asusai d abayaninka na mutum, hakkinka ne ka sirranta kalmar-shigarka. Kada ka rarraba shi. Idan kana amfani da kwafutar jama'a, ya kamata koda yaushe kullewa kafin barin shafin intanet ko wani aiki don kare masu amfani a bayanka daga damar bude bayaninka.
Inda ake Adanawa da Sarrafa Bayani
Z a a iya adanawa da sarrafa bayanan mutum da aka tattara a shafukan intanet da aiyuka na Microsoft a kasar Amurka ko kuma kowace kasa inda Microsoft ko madanganta, rassansa ko masu samar da aiki da ke gudanar da kayan aiki. Microsoft ta yarda da U.S.-EU Safe Harbor Framework da kuma U.S.-Swiss Safe Harbor Framework kamar yadda Ma’aikatar Kasuwanci ta Amirka ta gindaya dangane da abin da shafi tattara, amfani da kuma riƙe bayanai daga Yankin Tattalin Arzikin Turai, da kuma Switzerland. Don ƙarin masaniya game da shirin Safe Harbor, da kuma duba shahada, ziyarci http://www.export.gov/safeharbor/.
A ɓangaren shigar Microsoft shirin Safe Habor, muna amfani ne da TRUSTe, wani shirin wasu mai zaman kansa, wajen warware saɓani da kake da shi da ya shafi dokoki da kuma ayyukanmu. Idan za ka so tuntuɓar TRUSTe, ziyarci https://feedback-form.truste.com/watchdog/request.
Microsoft zai iya rikƙe bayaninka na mutum saboda dalilai mabambsnts, kamar don biyayya ga alƙawuranmu na shari’a, sasanta riciki, aiwatar da yarjejeniyoyinmu, sannan da in ya zama dole don samar da ayyuka. Don sanin yadda za ka shiga bayaninka na mutum, ziyarci Iso ga Bayaninka..
Cabje canje a Bayanan Sirrinmu
Za mu rika yawan sabunta bayanan sirrinmu don su dace da muradun abokan ciniki da kuma canje canje a aiyukanmu. Yayin da muka lika canje canje a wani bayanin, za mu sake duba kwanan watan "sabuntawar karshe" a saman bayanin. Idan akwai canje canje na zahiri a wani bayani ko a yadda Microsoft zai yi amfani da bayaninka na mutum, za mu sanar da kai kodai ta sananniyar hanyar lika sanarwa ta wadannan canje canje kafin su fara aiki ko kuma ta hanyar aika maka da sanarwa kai tsaye. Muna baka shawarar rika duba bayanan sirri na hajoji da aiyukan da ka ke amfani da su akai akai don sanin yadda Microsoft ke kare bayaninka.
Yadda za a Tuntube Mu
Microsoft Privacy, Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, Washington 98052 USA
Don neman reshen Microsoft a kasa ko yankinku, duba http://www.microsoft.com/worldwide/.
FTC Kare Tsre Sirri
Tsaro a gida
Trustworthy Computing